Mark 3

1Sai kuma ya sake tafiya cikin Majami’a sai ga wani Mutum mai shanyayyen hannu. 2Wadansu mutane suna kallonsa sosai, su gani ko zai warkar da shi a ranar Asabar. don su zarge shi.

3Yesu ya ce wa mai shanyayyen hanun “Ka tashi ka tsaya a tsakiyar kowa.” 4Sai ya ce wa mutane, “Ya dace a yi abu mai kyau aranar Asabar ko a yi mugunta; a ceci rai, ko a yi kisa? “Amma suka yi shiru.

5Sai ya dube su cikin fushi, yana bakin ciki da taurin zuciyar su, ya ce wa mutumin ka mikar da hanunka, sai ya mikar da hanunsa Yesu kuwa ya warkar da shi. 6Sai Farisiyawa suka fita da sauri zuwa wurin mutanen Hirudus suka shirya yadda za su kashe shi.

7Sai Yesu da almajiransa, suka tafi bakin teku. sai mutane dayawa suka bi shi, daga Galili da Yahudiya 8Daga Urushalima da Edom gaba da Urdun da kewayan Taya da Sidon, da baban taro, ya ji abinda yake yi. suka zo wurinsa.

9Ya tambayi almajiransa su shirya masa karamin jirgin ruwa domin yawan mutane, domin kada su murkushe shi. 10Ya warkar da mutane da yawa, yadda duk wadanda suke da cuttutuka suna kokari su taba shi.

11Duk sa’adda kazaman ruhohin suka ganshi, sai su durkusa a gabansa su yi ihu da karfi su ce, kai Dan Allah ne.” 12Ya umarce su da karfi kada su sa a san shi.

13Ya hau saman dutsen, ya kira wadanda yake bukar su, su zo wurinsa. 14Ya zabi guda goma sha biyu (ya kira su manzanni). Wadanda zasu kasance tare da shi, ya kuma aike su, su yi wa, azi, 15Ya kuma basu Ikon fitar da aljanu. 16Ya zabi guda goma sha biyu wato Saminu kuma yaba shi suna Bitrus.

17Yakubu dan Zabadi da Yahaya dan-uwan Yakubu wanda ya basu sunan Buwanarjis watau ‘ya’yan tsawa, 18da Andarawus da Filibus da Bartalamawus da Matta da Toma da Yakubu dan Halfa, da Taddawus da Saminu Ba-kananiye, 19da Yahuza Iskariyoti wanda zai bashe shi.

20Sa’adda ya shiga gida, Taron kuwa ya sake haduwa, har ya hana su cin abinci, 21Da iyalansa suka ji haka, sai suka fito sun kamo shi, saboda sun ce, “Ai, baya cikin hankalinsa “ 22Marubutan da suka zo daga Urushalima suka ce “Ai Ba’alzabuba ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.”

23Yesu ya kirawo su wurinsa ya ce da su cikin misalai, “Yaya shaidan zai iya fitar da shaidan? 24idan mulki ya rabu gida biyu ba zai tsayawa ba. 25Haka in gida ya rabu kashi biyu, gaba da kansa bai zai tsaya ba.

26Shaidan kuma in ya tayar wa kansa ya rabu, ba zai iya tsayawa ba, gama karshen sa ya zo kenan. 27Amma ba mai iya shiga gidan kakkarfan mutum ya kwace kayansa, ba tare da ya fara daure kakkarfan mutumin ba, sa’an nan kuma ya kwashe kayan gidansa.

28Hakika, ina gaya maku, dukan zunuban da mutane suka yi za a gafarta masu, da kowane irin sabon da suka furta, 29amma fa duk wanda yayi sabon Ruhun Mai Tsarki baza a gafarta masa ba ko kadan, ya zama mai zunubi har abada.” 30“Yesu ya fadi wadannan abubuwa domin suna cewa yana da ba kazamin ruhu,”

31Sa’an nan uwatasa, da “Yan’uwansa suka zo suna tsaye a waje. sai suka aika masa, suna kuma umurtar sa ya zo. 32Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka yi magana da shi da cewa, ga uwarka da yan-uwanka suna nan a waje, suna nemanka.”

33Ya amsa masu, “Dacewa su wanene uwa-ta da “yan’uwa na? “ 34Sai ya waiwayi wadanda suke zaune kewaye da shi, yace, “Ga uwa-ta da yan-uwana anan! Gama duk wanda ke yin abin da Allah yake so, shine dan’uwana da yar, uwata, da kuma uwa-ta.”

35

Copyright information for HauULB